- Gwamna Dauda Lawal Dare ya karrama Hajiya Aishatu Nahuce kan irin abin kirki da ta yi a Saudiyya
- Nahuce ‘yar asalin karamar hukumar Bangudu ta tsinci Dala 80,000 kimanin N64, 240,000 a kasa mai tsarki
- Kakakin gwamnan, Sulaiman Bala ya bayyana cewa gwamnan ya karrama Hajiyar ce tare da rakiyar dukkan sarakuna jihar
Jihar Zamfara – Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal Dare ya karrama Hajiya Aishatu Nahuce da ta mayar da kudin da ta tsinta a Saudiyya.
Hajiya Aishatu ‘yar asalin karamar hukumar Bungudu ta tsinci Dala 80,000 kimanin N64,240,000 a kasa mai tsarki inda ta mika su ga hukumar alhazai ta jihar da ke Saudiyya.
A cikin wata sanarwa da kakakin gwamnan, Sulaiman Bala ya fitar ya ce gwamnan ya karrama Hajiyar ce tare da rakiyar dukkan sarakunan jihar da aka gudanar a gidan gwamnatin jihar, Channels TV ta tattaro.
Assha: Wata Amarya Ta Datse Mazaƙutar Angonta Kan Abu 1 a Jihar Katsina
Dare ya nuna farin cikinsa inda ya karrama ta saboda abin da ta yi
Gwamnan ya nuna jin dadinsa yadda matar ta nuna tsantsar gaskiya inda ya ce daukacin mutanen jihar na alfahari da ita, cewar PM News.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A cewarsa:
“Daukacin mutanen jihar Zamfara na alfahari da abin da Hajiya Aishatu ta yi a Saudiyya, hakan ya kara mutunta sunan jihar Zamfara.“Wannan karramawar tamu ce ba ta Hajiya Aishatu ba, ta rubuta sunanta a cikin littafin tarihi, ana tsammanin haka daga dukkan wani Musulmi a kasar Saudiyya.“Wannan abin alfahari ne da kwaikwayo daga Hajiya Aishatu, ina tabbatar muku ba kowa ne zai samu wannan kudade ya mayar ba."Gwamnan ya yi alkawarin taimakon Nahuce
Ya kara da cewa:
“Gwamnatin jihar Zamfara za ta yi abinda ya dace don taimakon iyalan Hajiya Aishatu, Shugaba Bola Tinubu ma zai karrama ta akan wannan abin kirki da ta yi.”Hukumar DSS Ta Magantu Kan Rigimar Da Ta Faru Kan Emefiele a Kotu, Ta Faɗi Matakin Da Za Ta Ɗauka
Tun farko, Sarkin Bangudu, Alhaji Hassan Attahiru yayin gabatar da Hajiya Aishatu ya ce wannan abin da ta yi zai kara wa mutanen Zamfara mutunci a idon duniya.
Hajiya Aishatu a bayaninta ta bayyana yadda abin ya kasance a kasa mai tsarki yayin gudanar da aikin hajjin bana, cewar Leadership.
Mahajjaciyar Najeriya Ta Tsinci Miliyan 56 A Saudiyya, Ta Mayarwa Mai Shi
A wani labarin, Hajiya Aishatu Nahuce ta tsinci $80,000 yayin aikin hajji a Saudiyya.
Matar ta yi abin a yaba yayin da ta mayarwa mai shi, wanda akalla kudin ya kai Naira miliyan 64.
Mutane da dama sun yabawa matar ganin yadda a yanzu ba kowa ne zai iya aikata abin da ta aikata ba.
Asali: Legit.ng
ncG1vNJzZmigkarAonrLnp6irF6jtHC6xLCqaGllaYNzg5dmnrCZnaOur3nZmqSfmaKWerqtjKSYq6qRoq5uusChrJydXZmubsDAZqSasZGneqWtjJ2YpaecnrtuwNKipa2tp5Z6onnSmqydoamurnA%3D